Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya la'anci mai yin ƙarin gashi da wacce ta nemi a yi mata ƙarin gashi, da mai yin zane a jiki da wacce ta nemi a yi mata
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya la'anci mai yin ƙarin gashi da wacce ta nemi a yi mata ƙarin gashi, da mai yin zane a jiki da wacce ta nemi a yi mata.
Explanation
Benefits
Haramcin taimakekeniya akan saɓo.
Hani daga canja halittar Allah; domin cewa shi ƙarya ne da kuma algus.
Halaccin tsinewa wanda Allah da manzonSa suka tsinewa ta hanyar gamewa.
Ɗaura Baruka (wigi) a wannan zamanin yana shiga cikin ƙarin gashin da aka haramta, ita abar haramtawa ce dan abinda ke cikinta na kamanceceniya da kafirai da algus da kuma maguɗi.
AlKhaɗɗabi ya ce: kaɗai narko mai tsanani ya zo a cikin waɗannan abubuwan; dan abinda ke cikinsu na algus da yaudara, da a ce an yi rangwame a cikin wani abu daga garesu da ya zama tsani zuwa neman halatta waninsu na nau'ikan algus, haka kuma dan abinda ke cikinsu na canja halitta, akwai nuni zuwa ga haka a cikin hadisin Ibnu Mas'ud da faɗinsa: "Masu canja halittar Allah", Allah ne mafi sani.
AlNawawi ya ce: Hakan haramun ne akan wacce ta yi da wacce aka yi wa, kuma gurin da aka zana ɗin yana zama najasa, idan zai yi wu a gusar da shi da magani to wajibi ne, idan ba zai yi wu ba sai da ciwo, idan ya ji tsoron ɓaci ko rasa gaɓa ko amfanin (gaɓar) ko wani abu mai muni a cikin gaɓar a zahiri to gusar da shi ba ya wajaba, idan ya tuba wani laifi ba zai ragu daga gare shi ba, idan ba ya jin tsoron wani abu daga hakan to gusar da shi ya wajaba kuma zai yi saɓo idan ya jinkirta gusarwar.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

