HadeethEnc · 1.25.0
Allah ba Ya duba zuwa ga namijin da ya zo wa wani namiji ko wata mace ta dubura
Available translations
Choose an available translation of this Hadeeth
01
Hadeeth text
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Allah ba Ya duba zuwa ga namijin da ya zo wa wani namiji ko wata mace ta dubura".
02
Explanation
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana narko mai tsanani da cewa Allah ba Ya duba duban rahama zuwa namijin da ya zo wa namiji ta duburarsa ko mace ta duburarta, kuma hakan laifi ne babba daga cikin manyan laifuka.
03
Benefits
Zakkewa namiji ga namiji - shi ne liwaɗi - yana daga manyan zunubai.
Zakkewa mace ta duburarta yana daga manyan zunubai.
(Allah ba Ya duba) wato duba na rahama da tausayi, ba ana nufi da shi cewa: Duba gamamme ba; domin Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - wani abu ba ya ɓoyuwa gare Shi kuma wani abu ba ya fakuwa daga ganinSa.
Waɗannan ayyukan suna daga manyan (ayyukan) alfasha kuma mafi haɗarinsu akan mutuntaka; dan abinda ke cikinsu na saɓawa nagartacciyar ɗabi'a ta mutuntaka, da ƙarancin zuriya, da ɓa ta rayuwar auratayya, da dasa ƙiyayya da gaba, da afkawa a wuraren ƙazanta.

Attribution
[Tirmizi da Nasa'i a cikin Al-kubra ne Suka rawaito shi]
Categories
Share
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares