Cewa wani mutum ya tambayi Manzon Allah -tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi: Wanne aiki ne ya fi a Musulunci? ya ce: "Ka ciyar da abin ci, ka yi sallama ga wanda ka sani da wanda baka sani ba
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abdullahi Dan Amr - Allah Ya yarda da su -: Cewa wani mutum ya tambayi Manzon Allah -tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi: Wanne aiki ne ya fi a Musulunci? ya ce: "Ka ciyar da abin ci, ka yi sallama ga wanda ka sani da wanda baka sani ba".
Explanation
Na farko: Yawaita ciyar da abin ci ga talakawa, sadaka da kyauta da saukar bako da walima za su shiga ciki, falalar ciyarwa tana karfafa alokutan yunwa da tsadar farashi.
na biyu: Yin sallama ga kowanne musulmi, ka san shi ko ba ka san shi ba.
Benefits
Sallama da ciyar da abinci suna daga mafifitan ayyuka; Dan falalarsu da bukatuwar mutane garesu a kowanne lokaci.
Da wadannan dabi'un ne kyautatawa take taruwa da fada da aikatawa, kuma ita ce mafi cikar kyautatawa.
Wadannan dabi'un a cikin abinda yake rataya ne na mu'amalantar musulmai a tsakaninsu, akwai wasu dabi'un na mu'amalantar bawa ga Ubangijinsa.
Farawa da sallama abin kebancewa ne tsakanin musulmai, ba'a Farawa kafirai da sallama.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

