Haƙiƙa na faɗi wasu kalmomi huɗu a bayanki, sau uku, da za'a auna su da abin da kika faɗa a yau da sun rinjaye su
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Nana Juwairiyya Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita -: Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya fita daga wurinta da sassafe yayin da ya yi sallar Asuba, alhali tana wurin sallarta, sannan ya dawo bayan hantsi ya daga, alhali tana nan a zaune, sai ya ce: «Ba ki gusheba a kan halin da na barki a kansa?» Ta ce: Eh, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: «Haƙiƙa na faɗi wasu kalmomi huɗu a bayanki, sau uku, da za'a auna su da abin da kika faɗa a yau da sun rinjaye su: Tsarki ya tabbata ga Allah da godiyar Sa, adadin halittar Sa, da yardar kanSa, da nauyin Al’Arshin Sa, da tawadar kalmomin Sa).
Explanation
Benefits
Zikiri yana fifita, sashinsa ya fi sashi.
Nawawi ya faɗa akan faɗinsa (tsarki ya tabbatarwa Allah da godiyrSa tawadar kalmominSa): Abin nufi shi ne kai matuƙa da shi a cikin yawa; domin cewa shi a farko ya ambaci abinda ƙididdiga mai yawa take iyakance shi na adadin halitta, sannan awon al’Arshi, sannan ya hau zuwa abinda shi ne mafi girma daga hakan kuma ya bayyanar game da shi da wannan, wato abinda ƙididdiga bata iya iyakance shi kama yanda ba'a iya iyakance ta.
Ibnul Kayyima ya ce: Abinda yake tsayuwa da zuciyar mai zikiri lokacin da yake cewa: Tsarki ya tabbata ga Allah da godiyarSa, adadin halittarSa... har zuwa ƙarshensa na saninSa da tsarkakeShi da kuma girmamaShi daga wannan gwargwadan abin ambata daga adadin shi ne mafi girma daga abinda yake tsayuwa da zuciyar mai faɗin: "Tsarki ya tabbata ga Allah" kawai.
Shiryarwa zuwa kalmomi masu tattarowa waɗanda suke ɗaukar lafuzza kaɗan, kuma akansu a bada falala mai yawa da kuma sakamako.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

