Mumini kakkarfa ya fi alkairi da soyuwa a wajen Allah sama da mumini rarrauna, akwai alkairi a kowanne,
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Mumini kakkarfa ya fi alkairi da soyuwa a wajen Allah sama da mumini rarrauna, akwai alkairi a kowanne, ka yi kwadayin yin abinda zai amfane ka, kuma ka nemi taimakon Allah, kada ka gaza, idan wani abu ya sameka kada ka ce: Dana aikata da kaza da kaza ya kasance, sai dai ka ce : Kaddarar Allah abinda Ya so zai aikata, domin cewa (da a ce) tana bude aikin Shaidan".
Explanation
Benefits
An so karfi a ayyuka; Domin yana faruwa ne daga fa'idar abinda ba ya faruwa da rauni.
Mutum ya kamata ya yi kwadayi akan abinda zai anfane shi, kuma ya bar abinda ba zai anfane shi ba.
Yana wajaba akan mumini ya nemi taimakon Allah a dukkanin al'amuransa, kuma kada ya dogara da kansa.
Tabbatar da hukunci da kaddara, kuma shi ba ya kore kokari a sabubba da kokari a neman alkairai.
Hani game da fadin "Da a ce" ta fuskar fushi a lokacin saukar musibu, da haramcin bijirewa hukunci da kaddara ga Allah - Madaukakin sarki -.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

