Za'a tashi mutane a ranar Lahira marasa takalma tsirara kuma marasa kaciya
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: «Za'a tashi mutane a ranar Lahira marasa takalma tsirara kuma marasa kaciya». Na ce: Ya Manzon Allah! mata da maza baki ɗaya sashinsu yana kallon sashi? Sai (Manzon Allah) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: «Ya A'isha, al'amarin ya fi tsanani a ce sashinsu yana kallon sashi».
Explanation
Benefits
Karfafawa cewa mutum ba zai afka cikin saɓo ba sai dai a halin rafkana; dan da zai tina girman wanda ya saɓawa ko uƙubarSa da bai rafkana ba daga tinaShi da kuma gode maSa da kyakkyawan bautarSa ko da ƙiftawar ido, saboda haka zaka ga ma'abota taron alƙiyama sun shagalta da kawunansu sashinsu ba ya kallon sashi.
Tsananin kunyar mata a zamanin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, wannan Nana A'isha ce - Allah Ya yarda da ita - tana tambaya cikin kunya lokacin da ta ji cewa za'a tashi halitta tsirara maza da mata.
Sindi ya ce: Kowanne mutum ya shagalta da al'amarinsa kuma bai san halin ɗan'uwansa ba, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Kowane mutum daga cikinsu a wannan ranar sha'aninsa ya wadace shi} [Abasa: 37]. Babu wani da zai iya juyawa zuwa ga al'aurar wani.
Kaciya: Ita ga namiji ita ce: Yanke fatar da ta rufe hashafa, ta mace kuma ita ce: Yanke fatar da ke saman bigiren da azzakari yake shiga ya yi kama da ƙahon zakara.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

