Duk wanda ya zama yana da wani abin da ya zalinci ɗan uwansa da shi na mutuncinsa ne ko wani abu to ya yi ƙoƙarin warwarewa daga gare shi a yau, tun kafin lokacin da babu dinari ko dirhami
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Duk wanda ya zama yana da wani abin da ya zalinci ɗan uwansa da shi na mutuncinsa ne ko wani abu to ya yi ƙoƙarin warwarewa daga gare shi a yau, tun kafin lokacin da babu dinari ko dirhami, idan yana da wani aiki na gari za'a ɗauka daga cikin shi gwargwadan zalincinsa, idan ba shi da wasu kyawawan ayyuka za'a ɗauka daga munanan ayyukan ɗan'uwansa (da ya zalinta) sai a jibga masa su».
Explanation
Benefits
Kwaɗaitarwa akan yin gaggawa dan kuɓutar da kawuna daga abinda suka rataya da shi na haƙƙoƙi.
Ayyuka na gari zalintar mutane da cutar da su yana ɓata su kuma yana tafiyar da amfaninsu.
Haƙƙoƙin bayi Allah ba Ya gafarta su, sai ta hanyar mai da su ga masu su.
Dinari da dirhami sune tsani na jawo abubuwan amfani a duniya, amma a ranar Lahira to sai dai kyawawan ayyuka da munana kawai.
Wasu daga cikin malamai sun faɗa a cikin mas'alar Irbad: Idan wanda aka zalinta bai sani ba to babu buƙatuwar ya sanar masa, misali a ce ya zage shi a wani wuri daga cikin wurare kuma ya tuba, to a nan shi babu wata buƙatuwa ya sanar da shi, saidai babu bukatar ya sanar da shi , saidai ya nema masa gafara, kuma ya yi masa addu'a, ya yabi alherinsa a wuraran da ya zage shi a cikinsu, da haka ne zai warware daga gare shi .
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

