Wanda ya mari kunci, kuma ya yaga aljihuna, kuma ya yi ihu irin ta Jahiliyya to ba shi tare da mu
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abdullahi ɗan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya mari kunci, kuma ya yaga aljihuna, kuma ya yi ihu irin ta Jahiliyya to ba shi tare da mu".
Explanation
Na farko: Wanda ya mari kundukuki (kumatu) an keɓanci kundukuki dan kasancewarsa shi ne galibi a hakan, inba haka ba marin sauran fuska yana shiga cikin hanin.
Na biyu: Yaga abnida ake buɗewa daga tufa dan kai ya shiga cikinsa saboda tsananin baƙin ciki.
Na uku: Yin kururuwa irin ta mutanen Jahiliyya kamar ihu da kaico da halaka da kukan mutuwa da wanin hakan.
Benefits
Wajabcin haƙuri akan masifa, da haramta fushi akan ƙaddarorin Allah masu raɗaɗi, da bayyanar da hakan: Da kukan mutuwa ko aske kai ko yaga riga ko wanin hakan.
Haramcin kwaikwayon Jahiliyya da al'amuransu waɗanda mai shari'antawa bai tabbatar da su ba.
Babu laifi akan damuwa da hawaye, shi ba ya kore haƙuri akan hukuncin Allah - Maɗaukakin sarki -, kawai shi tausayi ne Allah Ya sanya shi a cikin zukatan makusanta da masoya.
Yarda da hukuncin Allah ya wajaba akan musulmi, idan bai yarda ba to haƙuri wajibi ne a kansa.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

