Diga-digan bawa ba za su gusheba a ranar Alkiyama har sai an tambaye shi game da rayuwarsa a me ya karar da ita, da kuma iliminsa me ya aikata da shi, da dukiyarsa daga ina ya samota kuma a me ya ciyar da ita, da jikinsa wanne aiki ya yi da shi
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abu Burzata Al-Aslami - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce : "Diga-digan bawa ba za su gusheba a ranar Alkiyama har sai an tambaye shi game da rayuwarsa a me ya karar da ita, da kuma iliminsa me ya aikata da shi, da dukiyarsa daga ina ya samota kuma a me ya ciyar da ita, da jikinsa wanne aiki ya yi da shi".
Explanation
Na daya: Rayuwarsa a me ya karar da ita?
Na biyu: Iliminsa shin ya neme shi ne saboda Allah? kuma ya yi aiki da shi? kuma shin ya isar da shi ga wanda ya cancance shi?
Na uku: Dukiyarsa daga ina ya samota shin daga halal ne ko daga haram? kuma a me ya ciyar da ita a abinda zai yardar da Allah ne, ko a abinda zai fusatar da Shi?
Na hudu: Jikinsa da karfinsa da lafiyarsa da samartakarsa a me ya yi da shi ya kuma aiwatar da shi?
Benefits
Ni'imomin Allah ga bayinSa masu yawa ne kuma za'a tambaye shi daga ni'imar da ya kasance a cikinta, to ya wajaba akansa ya sanya ni'imomin Allah a abinda zai yardar da Shi.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

