Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan goman ƙarshe ta shiga zai raya dare, zai farkar da iyalansa, zai yi ƙoƙari zai ɗaure gwabso
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan goman ƙarshe ta shiga zai raya dare, zai farkar da iyalansa, zai yi ƙoƙari zai ɗaure gwabso.
Explanation
Benefits
AlNawawi ya ce: A cikin wannan hadisin: Cewa an so a yi ƙari daga ibadu a cikin goman ƙarshe na Ramadan, kuma an so raya dararensa da ibadu.
Yana kamata ga bawa ya zama mai kwaɗayi akan iyalansa da umartarsu da yin ibada, kuma ya yi haƙuri akansu.
Aikata alherai yana buƙatuwa zuwa ƙudirin niyya da haƙuri da dagewa.
AnNawawi ya ce: Malamai sun yi saɓani a ma'anar (ya ɗaure gwabso) an ce: Shi ne ƙoƙari a cikin ibadu ƙari akan al'adarsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a waninsa, kuma ma'anarsa: Zage damtse a cikin ibadu, ana cewa; Na ɗaure gwabso na dan wannan al'amarin, wato: Na zage damtse gare shi na yi ƙoƙari, an ce: Shi kinaya ne game da nisantar iyali dan shagaltuwa da ibadu.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

