Kada ka kashe shi, domin cewa in ka kashe shi to shi yana matsayinka kafin ka kashe shi, kuma kai kana matsyinsa kafin ya fadi kalmarsa wacce ya fadeta
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Miƙdadu ɗan Amr mutumin Kindi - Allah Ya yarda da shi -: Cewa shi ya cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Shin kana ganin cewa idan na haɗu da wani mutum daga kafirai sai muka yi faɗa, sai ya daki ɗaya daga hannayena da takobi sai ya yanke shi, sannan ya fake dani da wata bishiya, sai ya ce: Na miƙa wuya ga Allah, shin zan kashe shi ya Manzon Allah bayan ya faɗeta? sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Kada ka kashe shi" sai ya ce: Ya Manzon Allah lallai cewa shi ya yanke mini ɗaya daga hannayena, sannan ya faɗi hakan bayan ya yanke mini shi? sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Kada ka kashe shi, domin cewa in ka kashe shi to shi yana matsayinka kafin ka kashe shi, kuma kai kana matsyinsa kafin ya fadi kalmarsa wacce ya fadeta".
Explanation
Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce masa: Kada ka kashe shi.
Sai ya ce ya Manzon Allah, lallai cewa shi ya yanke ɗayan hannayena, shin a tare da hakan ba zan kashe shi ba?
Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Kada ka kashe shi, domin cewa shi ya wayi gari jininsa haramun ne, domin cewa kai in ka kashe shi bayan musuluntarsa; to cewa shi a matsayinka ne wanda jininsa abin tsarewa ne da musuluntarsa, kuma kai kana matsayinsa abin halaratawar jini da ka kashe shi dan yin ƙisasi.
Benefits
Idan ɗaya daga kafirai ya Musulunta a tsakiyar yaƙi, to haƙiƙa an tsare jininsa, kuma kamewa daga gare shi ya wajaba sai dai idan saɓanin hakan ya bayyana daga gare shi.
Yana wajaba akan musulmi da son ransa ya zama bi ne ga shari'a badan ƙabilanci ko ɗaukar fansa ba.
Ibnu Hajar ya ce: Halaccin tambaya daga (mas'aloli) masu rintshi kafin afkuwarsu dan gini akan rinjayar da cewa ƙissar ba ta afku ba, amma abinda aka ruwaito daga wasu daga magabata daga ƙin hakan to shi abin ɗauka ne akan abinda afkuwarsa yake ƙaranta, amma abinda afkuwarsa yake yi wuwa a al'ada to an shara'anta tambaya game da shi dan a sani.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

