An bijiro min da aljanna da wuta ban ga kamar abinda na gani yau ba na alheri da sharri, da kun san abinda na sani da kun yi dariya kaɗan kuma kun yi kuka da yawa
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wani abu ya kai ga manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da sahabbansa, sai ya yi huɗuba ya ce: "An bijiro min da aljanna da wuta ban ga kamar abinda na gani yau ba na alheri da sharri, da kun san abinda na sani da kun yi dariya kaɗan kuma kun yi kuka da yawa" ya ce: Babu wani yini da ya taɓa zowa sahabban manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - mafi tsanani kamar wannan yinin, ya ce:
Sai suka rufe kawunansu suna ruri, ya ce: Sai Umar ya miƙe sai ya ce: Mun yarda da Allah a matsayin Ubangiji, da musulunci a matsayin addini, da (Annabi) Muhammad a matsayin annabi, ya ce: Sai wani mutum ya miƙe sai ya ce: Waye babana? ya ce: "Babanka shi ne wane", sai wannan ayar ta sauka: {Yaku waɗanda suka yi imani kada ku tambayi wasu abubuwa idan suka bayyana gareku zasu munana muku}.
[al-Ma'ida: 101].
Explanation
Haka (bantaɓa ganin) mafi sharri mafi yawa daga abinda na gan shi a cikin wuta a yau ba, da kun ga abinda na gani, kuma kun san abinda na sani daga abinda na gan shi a yau da kafin yau da kun ji tsoro, tsoro mai yawa, da dariyarku ta ƙaranta, kuma kukanku ya yawaita. Anas - Allah Ya yarda da shi -: Wani yini bai taɓa zo wa sahabbansa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ba - mafi tsanani daga wannan yinin ba, sai suka rufe kawunansu alhali gunji na kuka yana fita daga hanci saboda tsananin kuka. Sai Umar - Allah Ya yarda da shi - ya miƙe sai ya ce: "Mun yarda da Allah a matsayin Ubangiji, da musulunci a matsayin addini, da (Annabi) Muhammad a matsayin annabi". Ya ce: Sai wancan mutumin ya miƙe, sai ya ce: Waye babana?
Ya ce: "Babanka shi ne wane". sai (aya) ta sauka: {Yaku waɗanda suka yi imani kada ku yi tambaya game da wasu abubuwa idan suka bayyana gareku zasu munana muku}. [al-Maa'ida: 101].
Benefits
Tasirantuwar sahabbai - Allah Ya yarda da su - da wa'azin, da tsananin tsoronsu daga uƙubar Allah - Mai girma da ɗaukaka -.
An so rufe fuska a lokacin kuka.
AlKhaɗɗabi ya ce: Wannan hadisin ga wanda ya yi tambaya ne dan ɗorawa kai da kuma ta'annuiti a cikin abinda babu buƙatuwa zuwa gare shi, amma wanda ya yi tambaya dan wata larura shi ne cewa wata mas'ala ta faru gare shi sai ya yi tambaya game da ita to babu laifi ko zargi a kansa.
Kwaɗaitarwa akan daidaituwa akan biyayya ga Allah, da nisanta daga saɓon Allah, da tsayuwa a iyakokin Allah.
A cikinsa akwai halaccin yin fushi a lokacin wa'azi da kuma koyarwa.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

