HadeethEnc · 1.25.0
Babu Zakka a kasa da Ukiyya Biyar , ko kuma kasa da Rakuma Biyar, ko kasa da Buhu biyar.
Available translations
Choose an available translation of this Hadeeth
01
Hadeeth text
Daga Abu Sa'id Al'khudri -Allah ya yarda da shi- ya ce Manzon Allah - Tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce : "abu Zakka a kasa da Ukiyya Biyar , ko kuma kasa da Rakuma Biyar, ko kasa da Buhu biyar."
02
Explanation
Zakka: Yalwatawa ce tsakanin Mawadata da Mabukata, Kuma don haka ne ma ba'a karba daga wanda kudinsa basu taka kara sun karya ba don ba'a daukarsa Mawadaci.To kuma Sharia ta bayyana Mafi karancin abinda ya Wajaba ayi Zakka a kansa, amma kuma Duk wanda ya Mallaki kasa da Mafi karancin Haddin Zakka, to cewa shi Mabukaci ba'a karbar komai daga Wurinsa, to Ma'abocin Azurfa, Bai wajaba akansa Zakka har Sai ya kasance yana da Ukiyya biyar, kuma Ukiyya ita ce Dirhami Arba'in, to sai ya kasance Nisabin Zakkarsa a ciki Dirhami Dari biyu, wanda yayi daidai da Gram Dari biyar da Casa'in, kuma Mai zakkar Rakumabata wajaba akansa ba, har sai yana da Rakuma Biyar ko sama da haka, kuma kasa da haka babu zakka a ciki. kuma Mai Zakkar kayan Gonababu zakka a kansa sai ta kai Buhu biyar, kuma Buhu shi ne kwano Sittin, to sai ya kasance Nisabinsa shi Kwano Dari Uku.
Attribution
[Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]
Categories
Share
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

