Ina ganin mafarkenku haƙiƙa sun haɗu a bakwan ƙarshe, duk wanda ya kasance zai yi kardadonsa to ya yi kardadonsa a bakwan ƙarshe
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Ɗan Umar Allah Ya yarda da su: Cewa wasu mazaje daga sahabban Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - an nuna musu daren Lailatul-ƙadr a cikin mafarki a bakwan ƙarshe, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ina ganin mafarkenku haƙiƙa sun haɗu a bakwan ƙarshe, duk wanda ya kasance zai yi kardadonsa to ya yi kardadonsa a bakwan ƙarshe".
Explanation
Benefits
Daga hikimar Allah da rahamarSa cewa Ya ɓoye wannan daren dan mutane su yi ƙoƙari a cikin ibada, dan nemansa, sai ladansu ya yi yawa.
Lailatul-ƙadr a cikin goman ƙarshe na Ramadan, kuma ya fi (samun) ƙauna a bakwan ƙarshe daga gare shi.
Daren Lailatul-ƙadr ɗaya ne daga dararen goman ƙarshe na Ramadan, shi ne daren da Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya saukar da AlKur'ani a cikinsa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, kuma Ya sanya wannan daren ya fi wata dubu a albarkarsu, da girman darajarsu, da tasirin aiki na gari cikinsu.
An anbace shi (Lailatul-ƙadr) da w (Dal) ɗauri da hakan, kodai daga ɗaukaka ne sai a ce: Wane mai girman daraja ne, sai raɓa daren ya zama daga raɓawar abu ne zuwa siffarsa, wato dare maɗaukaki, yana nufin cewa shi mai girman daraja ne a ɗaukaka da bunƙasa da matsayi har zuwa ƙarshensa, (Lallai ne mu Mun saukar da shi a cikin wani dare mai albarka) [al-Dukhan: 3], ko kuma daga ƙaddarawa ne; Sai raɓawarsa zuwa gareshi ta zama daga raɓawar Zarfi ne zuwa abinda ya tattaroshi, wato wannan daren wanda ƙaddara abinda yake gudana cikin shekara yake kasancewa a cikinsa, (A cikinsa ne ake rarrabe kowane al'amari abin hukuntawa)) [al-Dukhan: 4].
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

