Lallai Shaidan yana gudu a jikin Mutum kamar yadda jini yake gudu a jikinsa, kuma inajin tsoron kada ya jefa wani sharri a cikin zukatanku ko ya fadi wani abu
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Safiyya Yar Huyai zuwa ga Annabi: "Annabi ya kasance yana i'itikafi sai nazo na ziyarce shi da daddare, sai mukai magana sannan na koma, sai ya tashi don ya rakani, kuma dakinta ya kasance a gidan Usama Dan Zaid, to sai sai wasu Mutane biyu suka wuce daga Mutanen Madina, yayin da suka ga Annabi sai sukai sauri sai Annabi ya ce musu, kuyi a hankali; ai matata Safiyya Yar huyayi ce, sai Suka ce tsaki ya tabbata ga Allah ya Manzon Allah, sai ya ce "ai lallai shaidan yana yawo ajikin Mutum ne kamar yadda jini yake yawo, kuma ina tsoron kada ya jefa wani abu a zuciyarku na sharri, ko ya ce wani abu daban" a wata riwayar kuma "Cewa ita tazo ta ziyarce shi a wajen I'itikafin sa a Masallaci, a goman karshe na Azumi to tai masa Magana wani dan lokaci, sannan ta tashi don ta tafi sai Annabi ya tashi tare da ita don ya raka ta har sai da ta isa kofar Masallaci dai dai kofar Ummusalama" sannan ya fadi Ma'anar wannan Hadisin.
Explanation
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

