Ya ku mutane ! Lallai Allah Mai tsarki ne ba Ya karba sai mai tsarki, kuma Allah Ya umarci muminai da abinda Ya umarci Manzanni da shi
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ya ku mutane ! Lallai Allah Mai tsarki ne ba Ya karba sai mai tsarki, kuma Allah Ya umarci muminai da abinda Ya umarci Manzanni da shi, sai Ya ce:
{Ya ku Manzanni ku ci daga tsarkaka kuma ku aikata aiki na gari, lallai cewa Ni Masani ne da abinda kuke aikatawa}.
[al-Mu'uminun: 51] .
Kuma Ya ce: {Ya ku waɗanda suka yi imani ku ci daga tsarkakan abinda muka azirta ku}. [al:Baƙara: 172]. Sannan ya ambaci mutumin da yake tsawaita tafiya kansa ya cukurkuɗe, jikinsa ya yi ƙura, yana ɗaga hannayensa sama: Ya Ubangiji, ya Ubangiji, abin cinsa haramun ne, abin shansa haramun ne, abin ɗaurawarsa haramun ne, an shayar da shi da haram, to tayaya za'a amsa masa ga hakan?".
Explanation
Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya gargaɗar daga cin haram wanda yake ɓata aiki kuma yake hana karɓarsa duk irin kokarin da ya yi na sabubban karɓar na zahiri; daga cikinsu:
Na farko: Tsawaita tafiya ta fuskokin ayyukan ɗa'a kamar hajji da jihadi da sada zumunci da wanin hakan.
Na biyu: Cukurkuɗar gashi dan rashin taje shi, wanda launinsa ya canja da launin tufansa daga turɓaya, shi mabuƙaci ne.
Na uku: Yana ɗaga hannayensa sama da addu'a.
Na huɗu: Yana tawassuli zuwa ga Allah da sunayenSa kuma yana nacewa a cikin hakan (yana cewa): Ya Ubangiji ya Ubangiji!
A tare da waɗannan sabubban na amsar addu'a ba'a saurare shi ba; hakan saboda abin cinsa da abin shansa da abin ɗaurawarsa haramun ne, kuma an shayar da shi da haram, to ya nisanta a amsa wa wanda wannan ita ce siffarsa, to ta yaya za'a amsa masa?!
Benefits
Umarni da tsarkake aiki saboda Allah - Mai girma da ɗaukaka -, da bin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
Anfani da abinda yake ƙarfafa gwiwa akan aiki, inda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai Allah Ya umarci muminai da abinda Ya umarci Manzanni da shi", idan mumini ya san cewa wannan yana daga abubuwan da aka umarci Manzanni to cewa shi zai ƙarfafu zai ji ƙwarin gwiwa akan riko da shi.
Daga abubuwan da suke hana amsar addu'a (akwai) cin haram.
Daga cikin sabubban amsar addu'a (akwai) abubuwa biyar: Na farkonsu: Tsawaita tafiya dan abinda ke cikinta na karyewar zuciya wanda shi yana daga mafi girman sabubban amsa addu'a. Na biyu: Halin buƙatuwa. Na uku: Ɗaga hannaye zuwa sama. Na huɗu: Nacewa Allah da maimaita ambatan RububiyyarSa, kuma shi yana daga mafi girman abinda ake neman amsa addu'a da shi. Na biyar: Daddadan abin ci da abin sha.
Cin halal mai tsarki yana daga sabubba masu taimakawa ga aiki na gari.
AlƘali ya ce: Mai tsarki kishiyar mummuna ne, idan Allah Maɗaukakin sarki ya siffanta shi da shi ana nufi da shi cewa shi abin tsarkakewa ne daga dukkanin tawaya abin tsarkakewa daga aibuka, idan aka siffanta bawa da shi kai tsaye ana nufi da shi cewa shi mai tsiraita ne daga munanan ɗabi'u kuma mai siffantuwa da kishiyoyin hakan, idan aka siffanta dukiyoyi da shi ana nufin kasancewarta halal ce kuma tana daga zaɓaɓɓun dukiyoyi.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

