To ku haɗu akan abincinku, kuma ku ambaci sunan Allah akansa, za'a sanya muku albarka a cikinsa
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Wahshi ɗan Harb - Allah Ya yarda da shi -: Cewa su sun ce: Ya Manzon Allah, lallai mu mun kasance muna ci ba ma ƙoshi, ya ce: «Wataƙila kuna ci ne a rarrabe?» Ya ce: Eh. Ya ce: «To ku haɗu akan abincinku, kuma ku ambaci sunan Allah akansa, za'a sanya muku albarka a cikinsa».
Explanation
Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce musu: Wataƙila kuna rarrabuwa a lokacin ci; sai kowa ya ci shi kaɗai? Suka ce: Eh. Ya ce: To ku haɗu ku ci ba'a rarrabe ba, kuma ku ambaci sunan Allah a lokacin ci da faɗin: Bismillah (Da sunan Allah), za'a sanya muku albarka a cikinsa, kuma zaku ƙoshi.
Benefits
Rabuwa dukkaninta sharri ce, haɗuwa kuwa dukkaninta alheri ce.
Kwaɗaitarwa akan haɗuwa da kuma ambatan Allah a lokacin abinci.
Sindi ya ce: Da haɗuwa ne albarkatu suke sauka a cikin abin ci, kuma da ambatan Allah ne Shaiɗan yake hanuwa daga kaiwa ga abinci.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

