Misalin wanda yake ambatan Ubangijinsa da wanda ba ya ambatan Ubangijinsa, kamar rayayye ne da matacce
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Misalin wanda yake ambatan Ubangijinsa da wanda ba ya ambatan Ubangijinsa, kamar rayayye ne da matacce", lafazin Muslim kuma: "Misalin gidan da ake ambatan Allah a cikinsa, da gidan da ba'a ambatan Allah a cikinsa, kamar rayayye ne da matacce".
Explanation
Haka nan gidan da ake siffanta shi da rayayye idan mazaunansa sun kasance suna ambatan Allah, inba haka ba to shi mataccen gida ne, saboda barin mazaunansa daga ambatan Allah; idan an wawaita mamaci da matacce a cikin siffanta gida kawai ana nufi da shi mazaunin gidan.
Benefits
Zikiri shi ne rayuwar rai, kamar yadda rai rayuwar jiki ne.
Daga shiryarwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - buga misali dan kusanto da ma'anoni.
Al-Nawawi ya ce: A cikinsa akwai kwaɗaitarwa akan ambatan Allah - Maɗaukakin sarki - a cikin gida, kuma cewa kada a wofantar da shi daga zikiri.
Al-Nawawi ya ce: Kuma a cikinsa cewa tsawon rayuwa a cikin ɗa'a falala ce koda mamacin yana cirata zuwa alheri; domin rayayye zai risku da shi kuma zai ƙaru a kansa da abinda ya aikata shi na ayyukan ɗa'a.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

