Akan me zamu yi maka caffa? ya ce: "Akan ku bautawa Allah kuma kada ku sanya wa Allah wani abun tarayya da Shi, da salloli biyar, ku bi - sai ya boye wata kalma boyayya - kada ku tambayi mutane komai
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abu Muslim Al-Khaulani ya ce: Masoyi amintacce ya zantar dani, amma shi to masoyi ne gareni, amma shi a wajena to amintaccene, Awf Dan Malik Al-Ashja'i - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Mun kasance wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - (Mu) tara ko takwas ko bakwai, sai ya ce: "Shin ba kwa yi wa Manzon Allah caffa ba?" mun kasance farkon yin caffa (mubaya’a) sai muka ce: Hakika mun yi maka caffa ya Manzon Allah, sannan ya ce: "Shin bakwa yi wa Manzon Allah caffa ba?" sai muka ce: Hakika mun yi maka caffa ya Manzon Allah, sannan Ya ce: "Shin bakwa wa Manzon Allah caffa ba?" Ya ce: Sai muka shimfida hannayenmu muka ce: Hakika mun yi maka caffa ya Manzon Allah, Akan me zamu yi maka caffa? ya ce: "Akan ku bautawa Allah kuma kada ku sanya wa Allah wani abun tarayya da Shi, da salloli biyar, ku bi - sai ya boye wata kalma boyayya - kada ku tambayi mutane komai" Hakika na ga sashin wadancan mutanan bulalar dayansu tana faduwa, amma ba ya tambayar wani ya miko masa.
Explanation
Na farko: Bautar Allah Shi kadai ta hanyar riko da umarninSa, da nisantar haninSa, kuma kada su hada wani abu daShi.
Na biyu: Tsaida salloli biyar na wajibai a yini da dare.
Na uku: Ji da bi da aikin alheri ga wanda ya jibinci al'amarin musulmai.
Na hudu: Kai dukkanin bukatunsu ga Allah da rashin tambayar mutane wani abu daga garesu, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi kasa-kasa da sautinsa da su.
Hakika sahabbai - Allah Ya yarda da su - sun yi aiki da abinda suka yi caffa akansa, har maruwaicin Hadisin ya ce: Hakika na ga wasu daga wadancan sahabban bulalar dayansu tana faduwa kasa , amma ba ya tambayar wani ya miko masa ita, kai yana sauka yana daukarta da kansa.
Benefits
Tambayar da aka hana: Tambaya mai alaka da al'amura na duniya, ba ta hado tambaya game da ilimi da al'amuran Addini ba.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

