An anbaci wani mutum da ya yi bacci a darensa har saida ya wayi gari a wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ya ce: "Wancan wani mutum ne wanda Shaiɗan ya yi fitsari a cikin kunnuwansa, ko ce ya yi: A cikin kunnensa
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abdullahi ɗan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: An anbaci wani mutum da ya yi bacci a darensa har saida ya wayi gari a wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ya ce: "Wancan wani mutum ne wanda Shaiɗan ya yi fitsari a cikin kunnuwansa, ko ce ya yi: A cikin kunnensa".
Explanation
Benefits
Tsoratarwa daga Shaiɗan wanda yake zama ga mutum a kan kowace hanya; dan ya tsare tsakaninsa da tsakanin ɗa'ar Allah - Mai girma da ɗaukaka -.
Ibnu Hajar ya ce: Faɗinsa: (Bai tashi zuwa sallah ba) abin nufi jinsi, kuma zai iya ɗaukar alƙawari, kuma ana nufin sallar dare ko (sallar) farillah da shi.
Al-Ɗaibi ya ce: An keɓanci kunne da anbato, duk da ido yafi dacewa da bacci, dan yin nuni zuwa nauyin bacci, domin cewa kunnuwa sune magangarar farkawa, kuma an keɓanci fitsari; domin cewa shi ya fi sauƙin shiga a cikin ciki, kuma mafi saurin zarcewa a cikin jijiyoyi, sai ya gadar da kasala a cikin dukkan gaɓɓai.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

