Ya Ubangiji ina roƙonKa shiriya da tsoron Allah, da kamewa, da wadata
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abdullahi ɗan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi ya kasance yana cewa: «Ya Ubangiji ina roƙonKa shiriya da tsoron Allah, da kamewa, da wadata».
Explanation
«Da tsoron Allah», ruko da umarni da nisantar hane-hane. «Da kamewa» kamewa daga abinda ba ya halatta kuma ba shi da kyau na magana ne ko aiki.
«Da wadatuwa» daga halitta, inda ba zai yi buƙatuwa ba zuwa ga wani inba Uabngijinsa - Mai girma da ɗaukaka ba -.
Benefits
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba ya mallakawa kansa wani amfani ko cutarwa, wanda yake mallakar hakan Shi ne Allah - Maɗaukakin sarki -.
Wanda yake mallakar amfani da cutarwa da shiryar da halitta Shi ne Allah Shi kaɗai, ba wani mala'ika makusanci ba kuma ba wani Annabi abin aikowa ko waninsu ba.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

