Lallai cewa mafi nauyin sallah a kan munafukai (ita ce) sallar Issha'i da sallar Asuba, da sun san abin da ke cikinsu da sun zo musu ko da da jan ciki ne
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lallai cewa mafi nauyin sallah a kan munafukai (ita ce) sallar Issha'i da sallar Asuba, da sun san abin da ke cikinsu da sun zo musu ko da da jan ciki ne, haƙiƙa na yi niyyar in yi umarni da sallah, sai atsai da ita, sannan in umarci wani mutum ya yi wa mutane sallah, sannan in tafi a tare dani da wasu mazaje a tare da su akwai ɗauri na itatuwa zuwa mutanen da ba sa zuwa sallah, sai na ƙona gidajensu da wuta".
Explanation
Haƙiƙa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi niyyar ya yi umarni a tsai da Sallah, sai ya sanya wani mutumin ya yi wa mutane limanci a maimakonsa, sannan ya tafi tare da shi akwai wanda zai ɗauki ɗauri na itatuwa zuwa mazajen da ba sa zuwa sallar jama'a, sai ya ƙona gidajensu da wuta; sabo da tsananin abin da suka aikata na laifi a hakan, - sai dai bai aikata ba - sabo da abinda ke cikin gidaje na mata da yara da babu-ruwansu da kuma wasunsu cikin masu uzuri waɗanda ba su da wani laifi.
Benefits
Munafukai ba sa nufin komai a ibadarsu sai riya da jiyarwa, ba sa zuwa sallah sai lokacin da mutane suke ganainsu.
Girman ladan sallar issha'i da Asuba tare da jama'a, kuma cewa su sun cancanci a zo musu ko da da rarrafe ne.
Kiyaye sallar Issha'i da Asuba kubuta ce daga munafunci, kuma ƙin zuwar musu yana daga siffofin maunafukai.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

