Idan ɗayanku ya ga wani abu a mafarkinsa da yake son sa to shi daga Allah ne, sai ya godewa Allah a kansa kuma ya bada labarin shi, idan kuma ya ga wanin hakan daga abinda yake ƙi, to kawai shi daga Shaiɗan ne, to sai ya nemi tsari daga sharrinsa, kuma kada ya fadawa kowa, to shi (mafarkin) ba zai cutar da shi ba
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abu Sa'id Khudri - Allah Ya yarda da shi - cewa shi ya ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Idan ɗayanku ya ga wani abu a mafarkinsa da yake son sa to shi daga Allah ne, sai ya godewa Allah a kansa kuma ya bada labarin shi, idan kuma ya ga wanin hakan daga abinda yake ƙi, to kawai shi daga Shaiɗan ne, to sai ya nemi tsari daga sharrinsa, kuma kada ya fadawa kowa, to shi (mafarkin) ba zai cutar da shi ba".
Explanation
Benefits
Abinda aka ambata a taƙaice a Babin kyakkyawan mafarki abubuwa ne uku: Shi ne ya godewa Allah akansa, kuma ya yi albushir da shi, kuma ya faɗawa wanda yake so shi banda wanda yake ƙinsa.
Abinda aka ambata a taƙaice daga ladabin mummunan mafarki abubuwa ne guda biyar: Ya nemi tsarin Allah daga sharrinsa, da kuma sharrin Shaiɗan, kuma ya yi tofi a hagunsa sau uku lokacin da ya farka daga baccinsa, kuma kada ya faɗawa kowa mafarkin, idan ya yi nufin komawa baccinsa to ya juya daga ɓangaren da yake akansa; to shi (mafarkin) ba zai cutar da shi ba.
Ibnu Hajar ya ce: Hikima a cikinsa cewa shi idan ya fadawa wanda ba ya ƙauna kyakkyawan mafarki zai iya fassara masa da abinda ba ya so kodai dan ƙiyayya ko dan hassada, kuma zai iya faruwa akan waccan siffar ko ya gaggautowa kansa baƙin ciki da takaici daga hakan, to sai aka umarce shi da barin fadawa wanda ba ya so saboda hakan.
Godiya a yayin faruwar ni'imomi, da sabuntuwar abubuwan buri, to hakan sababi ne na dawwamar su.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

