Ku yi gaggawa da jana'iza, idan ta gari ce to alheri kuke kaita gare shi, idan kuma koma bayan haka ne, to sharri ne kuke sauke shi daga wuyayenku
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annbai - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ku yi gaggawa da jana'iza, idan ta gari ce to alheri kuke kaita gare shi, idan kuma koma bayan haka ne, to sharri ne kuke sauke shi daga wuyayenku".
Explanation
Benefits
An ƙayyade gaggawar da idan mutuwar bata zama fuj'a ba wacce ake jin tsoron ta zama suma ce, to yana kamata kada a binneta har sai an tabbatar da mutuwarsa, ko ya zama akwai wata maslaha a cikin jinkirta shi, na yawaitar masallata, ko halartar 'yan uwansa, kuma ba'a jin tsoron ta ɓaci.
Kwaɗaitarwa akan yin gaggawa da jana'iza dan maslahar mamaci idan ya kasance ɗan aljanna ne, ko dan maslahar 'yan rakiya idan ya kasance ɗan wuta ne.
Nawawi ya ce: Ana ɗauka daga gare shi (wannan Hadisin) barin abokantakar da mutanen banza waɗanda ba mutanen kirki ba.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

