Tsarki ya tabbata ga Allah, lallai mumini ba ya zama najasa
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya haɗu da shi a wata hanya cikin hanyoyin Madina alhali shi yana da janaba, sai ya sulale ya tafi ya yi wanka, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bibiye shi, lokacin da ya zo masa sai ya ce: «Ina kake ya Abu Huraira?» sai ya ce: Ya Manzon Allah ka haɗu da ni alhali ni ina da janaba sai na ƙyamaci in zauna da kai har sai na yi wanka, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Tsarki ya tabbata ga Allah, lallai mumini ba ya zama najasa».
Explanation
Benefits
Tsarkakar mumini a raye ko a mace.
Girmama ma'abota falala, da ilimi, da salaha, da kuma zama da su akan yanayi mai kyau.
Halaccin neman izinin mai bi ga wanda ake bi idan zai tafi, haƙiƙa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - inkarin tafiyarsa ba tare da saninsa ba, hakan domin cewa neman izini yana daga cikin kyakkyawan ladabi.
Faɗin: Subhanal Lahi, a lokacin yin mamaki.
Halaccin zantar da mutum game da kansa da abinda ake jin kunya daga gare shi dan maslaha.
Kafiri najasa ne, sai dai najasarsa ta ma'ana ce dan munin aƙidarsa.
Nawawi ya ce: A cikin wannan hadisin akwai ladubba cewa malami idan ya ga daga wanda yake binsa wani al'amarin da yake jin tsoro a kansa wanda a cikinsa akwai saɓanin daidai to ya tambaye shi, kuma ya faɗa masa daidai, ya kuma bayyana masa hukuncinsa. Allah ne Mafi sani.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

