Lallai akwai halayyar daji ga wadannan dabbobin kamar dabbobin daji, wanda ya bijere muku daga cikinsu to ku yi haka da shi'
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga rafi'u ɗan Khadij - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Mun kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a Zul-hulaifa, sai yunwa ta kama mutane, sai suka samu raƙuma da tumakai, ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana cikin ƙarshen mutane, sai suka yi gaggawa, suka yanka, suka girka tukwane, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da tukwane, sai aka kifar da su, sannan ya raba, sai ya daidaita tumakai goma da raƙumi ɗaya sai wani raƙumi ya yi tsaurin kai, sai suka neme shi, sai ya gajiyar da su kuma a cikin mutanen dawakan kaɗan ne, sai wani mutum daga cikinsu ya sunkuyar da kibiya, sai Allah Ya tsare shi, sannan ya ce: "Lallai akwai halayyar daji ga wadannan dabbobin kamar dabbobin daji, wanda ya bijere muku daga cikinsu to ku yi haka da shi'.
Sai ya ce: wato rafi'u: Lallai mu muna jin kwadayi - ko muna jin tsron - makiya gobe, kuma babu wuka a tare da mu, shin zamu yanka ne da kara? ya ce: "Duk abinda ya zubar da jini, kuma aka ambaci sunan Allah akansa to sai ku ci shi, banda hakori da farce, kuma zan zantar da ku game da haka: Amma a hakori to kashi ne, amma farce to wuƙar mutanen Habasha ce".
Explanation
Benefits
Ladabatarwar shugaba ga talakawansa da kuma rundunarsa, haƙiƙa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ladabtar da su akan wannan gaggawar da kuma aikin da suka yi, kafin karɓar izninsa, sai sakamakonsu ya zama haramta musu abinda suka yi nufi.
Gaggawar amsawar sahabbai - Allah Ya yarda da su - ga umarnin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare su -.
Hana ɗaukar ganima har sai an rabata.
Adalci, musammanma agurin yaƙar maƙiya da kafirai; domin hakan yana daga sabubban nasara da rinjaye akan maƙiya.
Nawawi ya ce: Idan dabbar gida ta koma mai ɗabi'ar ta daji shi ne raƙumi ko saniya ko doki su yi taurin kai ko akuya ta gudu ko waninsu to shi ya zama kamar farauta ne, sai ya halatta ta hanyar harbi.
Yankan dabbobi yana wajaba dan cinsa ya halatta, dabbobi an sharɗanta musu abinda ke tafe: 1- Ya zama cinsa ya halatta. 2- Ya zama an samu iko a kansa, wanda ba'a samu iko a kansa ba to hukuncinsa shi ne hukuncin abin farauta. 3- Ya zama dabba ce ta sarari; amma dabbar ruwa to ba'a sharɗanta yanka gareta ba.
Sharuɗɗan ingancin yanka: 1-Cancantar mai yankan shi ne ya zama mai hankali mai mayyazewa kuma musulmi ko mazuwa littafi (Bayahude ko Banasare). 2- Ya ambaci sunan Allah a farkon yankan. 3- Ingancin abin yankan ga yanka shi ne abin yankan da za’a yi amfani da shi ya zama mai kaifi cikin kowane irin abu ne banda haƙori da farce. 4- Yankan ya zama gurin da ake yankawane ko kuma sokewa a abinda ake da iko akansa ta hanyar yanke maɗaciya da maƙogwaro da jijiyoyi.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

