Wani mutum ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alokacin yana kan mimbari, me kake gani a kan sallar dare, sai ya ce: «Biyu-biyu ce
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su -: Wani mutum ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alokacin yana kan mimbari, me kake gani a kan sallar dare, sai ya ce: «Biyu-biyu ce», idan ya ji tsoron (ɓullowar) Asuba sai ya sallaci raka'a ɗaya, sai ta yi masa wutirin abin da ya sallata» kuma shi ya kasance yana cewa «Ku sanya ƙarshen sallarku ta zama witiri» domin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da shi.
Explanation
Benefits
Cewa sallar dare ba'a ƙayyade ta da wani adadi ba; dan wawaitar da lafazin.
Nawawi ya ce: "Sallar dare da rana raka'a biyu-biyu ce", wannan abin ɗauka akan bayanin a bin da ya fi, shi ne ya yi sallama daga kowanne raka’oi biyu, kuma daidai ne nafilfilin dare da na rana an so mai sallah ya yi sallama daga kowanne raka’oi biyu.
Nawawi ya ce: A cikin wannan a kwai dalili akan sunna ita ce a sanya witiri a ƙarshen sallar dare, kuma lokacinsa yana fita ne da zarar alfijir ya ɓullo, shine mafi shahara a mazahabarmu, kuma da shi ne jumhur na malamai suka faɗa.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

