Gangaran a karatun Alƙur'ani yana tare da manyan mala'iku masu biyayya ga Allah, kuma wanda yake karanta Alƙur'ani kuma yake guragura a cikinsa yana mai shan wuya to yana da lada biyu
Choose an available translation of this Hadeeth
Hadeeth text
Daga Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Gangaran a karatun Alƙur'ani yana tare da manyan mala'iku masu biyayya ga Allah, kuma wanda yake karanta Alƙur'ani kuma yake guragura a cikinsa yana mai shan wuya to yana da lada biyu.
Explanation
Benefits
Alƙali ya ce: Ba wai ma'anarsa cewa wanda yake guragura gurin karanta shi ya fi gwani lada ba, kai gwani ya fi yawan lada; domin shi gwani yana tare da mala'iku matafiya kuma yana da ladaddaki mai yawa, kuma bai ambaci wannan matsayin ga waninsa ba, to kuwa ta yaya wanda bai kula da Littafin Allah - Maɗaukakin sarki - ba da haddace shi da kyautata shi da yawan karanta shi da dirayarsa hakikanin kulawarsa har ya zama gwani a cikinsa zai riske shi.
Ibnu Baaz ya ce: Wanda yake karanta Alƙur'ani alhali shi gwani ne a cikinsa, yana kyautata karatunsa, kuma yana haddarsa da kyau yana tare da mala'iku matafiya masu daraja, yana nufin: Idan ya kasance yana karanta shi a faɗa da aiki, ba wai mujarradin karantawar kawai ba, yana kyautata karatunsa kuma yana aiki da shi, shi yana tsaye da shi a lafazi da ma'ana.
Attribution
Categories
Share hadeeth
Sharing options · 0 Total shares

